<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>54</hymn_number>
<title>Tun da Farkon Hasken Safe LW54</title>
<lyrics>[V1]
 1)Tun da farkon hasken safe,
 Ko ka yi addu'a
 Cikin sunan Yesu Kristi,
 Ka yi roƙo har ka sami
 Taimakonka yau?

[V2]
 KORUS
 Yin addu'a dai zai ba mu
 Albarka ba iyaka.
 Sai ka riƙa yin addu'a
 Kowace sa'a.

[V3]
 2) Lokacin zuwan jaraba,
 Ko ka yi addu'a
 Don ka sami ikon Allah,
 Ruhunsa ya taimake ka
 Har da nasara?
 Korus

[V4]
 3) Lokacin da ka ke fushi
 Ko ka yi addu'a
 Kada Shaiɗan ya rinjaya
 Har ya sa ka yin tuntuƃe
 Cikin fushinka?
 Korus

[V5]
 4) Cikin tsanani da ba'a
 Ko ka yi addu'a,
 Ko ka jure, kana roƙo
 Har ka sami hutun ranka
 Cikin Almasihu?
 Korus</lyrics>
</song>